Sama Da Mutane 100 Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Iskar Gas A Ghana
Rahotanni daga kasar Ghana sun bayyana cewar sama da mutane 100 sun sami raunuka wasu daga cikinsu suna cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai sakamakon fashewar wata tankar daukar iskar gas a wani kamfani da ke yammacin kasar.
Kafar watsa labaran Africa News ta bayyana cewar lamarin ya faru ne a wani kamfani da ke yankin Takoradi da ke yammacin kasar Ghanan a daidai lokacin da wata tankar daukar iskar gas din ta fashe da kuma kamawa da wuta inda aka ce kusan mutane 200 sun sami raunuka ciki kuwa har da wasu 'yan kwana-kwana da suke aiki a wajen.
Har ila yau kamfanin dillancin labaran kasar Ghanan ya jiyo mataimakin babban jami'in hukumar 'yan kwana-kwanan ta kasar Ghanan Emmanuel Bonney yana tabbatar da faruwar wannan lamarin inda ya ce tankar ta kama da wuta din ne a daidai lokacin da take sauke iskar gas din a wani kamfani da ke yammacin kasar.
Cikin shekarun baya-bayan nan dai kasar Ghanan ta yi fama da irin wadannan fashewar na albarkatun man fetur inda a bara a shekara ta 2015 ma dai sama da mutane 150 suka kone yayin da wata fashewar da ta faru a wani gidan mai a kasar, kamar yadda a shekarar bara ma dai aka sami wata fashewar makamanciyar wannan lamarin da ya sanya shugaban kasar Nana Akoufo Addo kiran da a dau matakan da suka dace wajen kare faruwar hakan.