-
Tanzaniya : Hadarin Mota Ya kashe Yan Makaranta 29
May 06, 2017 13:09Rahotanni daga Tanzaniya na cewa yara yan makaranta akalla 29 ne suka rasa rayukansu a yayin wani hadarin mota a arewacin kasar.
-
An Kammala Taron Koli Kan Tattalin Arzikin Afrika
May 06, 2017 11:53An kammala taron koli na yini uku kan tattalin arzikin Afrika a birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu, inda aka tattauna kan batutuwa da suka shafi samar da ci gaba na bai daya da cinikayya tsakanin kasashen Afrika da kuma amfani da dabarun habaka tattalin arziki na zamani.
-
An Harbe Wani Minista Har Lahira A Somaliya
May 04, 2017 01:20Rahotanni daga Somaliya na cewa an harbe ministan kula da kwadigon jama'a na kasar, Abdullahi Siraji, har lahira a birnin Mogadisho.
-
Mali : An Kaiwa Sansanin MDD Hari A Tombuctu
May 04, 2017 01:20Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Mali, ta sanar da mutuwar sojinta guda da kuma jikkatar wasu tara a wani hari da aka kaiwa sansanninta a birnin Tombuctu.
-
WFP Ta Rage Yawan Abincin Da Take Badawa A CAR
May 04, 2017 01:19Hukumar samar da abinci ta duniya WFP ta ce, karancin kudi ya tilasta mata rage yawan abincin da take badawa ga iyalai a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
-
Polisario Ta Sanar Da Shirinta Na Tattauna Da Gwamnatin Moroko Kan Yammacin Sahara
May 02, 2017 06:46Kungiyar Polisario da ke neman 'yancin kan yankin Sahara ta sanar da aniyarta na fara tattaunawa da gwamnatin kasar Moroko kan yankin Yammacin Sahara da aka jima ana rikici kansa tsakaninsu.
-
Liberia : Ana Bincike Kan Bakuwar Cuta Da Ta Bullo
Apr 29, 2017 06:35Hukumomin Liberia da hukumar lafiya ta duniya na gudanar da bincike domin tantance bakuwar cutar data bulla a kasar wacce kawo yanzu ta hadassa mutuwar gomman mutane a cikin kwanaki biyar.
-
Tanzaniya : An Kori Ma'aikata 10,000 Saboda Difloma Na Bogi
Apr 29, 2017 06:34Shugaba John Magufuli na Tanzaniya ya sallami ma'aikata 10,000 daga bakin aiki saboda amfani da takardun difloma ko na aiki na karya.
-
Taron Masanan Kasashen Yammacin Afirka Kan Fada Da Ta'addanci A Kasar Togo
Apr 28, 2017 01:24A ci gaba da kokarin samo hanyoyin da za a bi wajen fada da ta'addanci a kasashen Yammacin Afirka, masana harkokin tsaro daga kasashe 10 na Yammacin Afirka sun gudanar da wani taro a birnin Lome, babban birnin kasar Togo don tattauna hanyoyin da za a bi wajen fada da ta'addancin.
-
ECOWAS Za Ta Janye Dakarunta A Guinea Bissau
Apr 26, 2017 06:36Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS za ta fara janye tawagar dakarunta ta a Guinea Bissau.