Liberia : Ana Bincike Kan Bakuwar Cuta Da Ta Bullo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19922-liberia_ana_bincike_kan_bakuwar_cuta_da_ta_bullo
Hukumomin Liberia da hukumar lafiya ta duniya na gudanar da bincike domin tantance bakuwar cutar data bulla a kasar wacce kawo yanzu ta hadassa mutuwar gomman mutane a cikin kwanaki biyar.
(last modified 2018-08-22T07:00:02+00:00 )
Apr 29, 2017 06:35 UTC
  • Liberia : Ana Bincike Kan Bakuwar Cuta Da Ta Bullo

Hukumomin Liberia da hukumar lafiya ta duniya na gudanar da bincike domin tantance bakuwar cutar data bulla a kasar wacce kawo yanzu ta hadassa mutuwar gomman mutane a cikin kwanaki biyar.

Bangarorin biyu sun ce bakuwar cutar mai hadassa zazzabi da amai da ciwan kai da gudawa ba tada wata alaka da cutar Ebola da ta bula a yammacin Afrika a cikin shekara 2013 zuwa 2016.

Ministan lafiya na kasar Sorbor George ya ce an binciki  samfarin jinin mutanen da suka kamu da cutar saidai babu wanda ya nuna alamun cutar Ebola.

Kawo yanzu dai za'a aikewa da samfarin jinin mutanen a kasashen waje domin tantance ko wacce irin cuta ce.

Alkalumman da hukumar lafiya ta duniya ta fitar sun ce mutane 19 suka kamu da bakuwar inda 11 daga cikinsu suka mutu.