ECOWAS Za Ta Janye Dakarunta A Guinea Bissau
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19824-ecowas_za_ta_janye_dakarunta_a_guinea_bissau
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS za ta fara janye tawagar dakarunta ta a Guinea Bissau.
(last modified 2018-08-22T07:00:01+00:00 )
Apr 26, 2017 06:36 UTC
  • ECOWAS Za Ta Janye Dakarunta A Guinea Bissau

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS za ta fara janye tawagar dakarunta ta a Guinea Bissau.

Wata sanarwa da kungiyar da kungiyar ta ECOWAS ta fitar ta ce bisa bukatar shugabannin kasashe mambobin kungiyar 15 za'a fara janye dakarun daga ranakun 28 zuwa 30 na wannan watan Afrilu da muke ciki.  

Matakin janye tawagar mai suna (Ecomib), ya biyo bayan ran gadin da mayan jami'an kungiyar ta ECOWAS suka kai a kasar ta Guinea Bissau.

An dai jibge dakarun tawagar ta Ecomib bayan juyin mulkin soji kasar na ranar 12 ga watan Afrilu 2012, domin tabbatar da tsaro a cikin tsarin mika mulki cikin ruwan sanyi.