Mali : An Kaiwa Sansanin MDD Hari A Tombuctu
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Mali, ta sanar da mutuwar sojinta guda da kuma jikkatar wasu tara a wani hari da aka kaiwa sansanninta a birnin Tombuctu.
Kawo yanzu dai ba'a kai ga bayyana asalin dan wacce kasa ce ba ya hallaka a harin.
A cikin sanarwar da ta fitar, tawagar ta MINUSMA ta yi Allah wadai da wannan hari, inda ta yi kira ga bangarori daban-daban da su gudanar da bincike don bankado wadanda suke da hannu a ciki.
Haka kuma tawagar ta MINISMA ta jaddada aniyarta ta ci gaba da tallafawa kasar Mali gami da al'ummarta wajen farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Tuni dai gungun kungiyoyin nan dake ikirarin kawo dauki ga musulinci da musulmai da aka kafa a baya bayan nan ya dauki alhakin kai harin.