WFP Ta Rage Yawan Abincin Da Take Badawa A CAR
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20044-wfp_ta_rage_yawan_abincin_da_take_badawa_a_car
Hukumar samar da abinci ta duniya WFP ta ce, karancin kudi ya tilasta mata rage yawan abincin da take badawa ga iyalai a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
(last modified 2018-08-22T07:00:03+00:00 )
May 04, 2017 01:19 UTC
  • WFP Ta Rage Yawan Abincin Da Take Badawa A CAR

Hukumar samar da abinci ta duniya WFP ta ce, karancin kudi ya tilasta mata rage yawan abincin da take badawa ga iyalai a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

WFP ta ce, kashi 7 cikin dari na kudin da take bukata ga shirinta na kai dauki cikin shekarar nan ta 2017 ne kadai ya samu.

Duk da dimbin bukatun da take da, kasar Afrika ta Tsakiya na daga cikin kasashen duniya masu fama da rikici da ake mantawa da su, kuma suke samun kudin agaji da bai taka kara ya karya ba.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya ce, rabin al'ummar kasar na bukatar agajin jin kai, sannan, sama da mutane miliyan biyu ne ke fama da yunwa.

Dujarric ya ce, hukumar WFP, na bukatar dalar Amurka miliyan 12.5 nan take, domin biyan bukatun gaggawa na mutanen dake cikin halin ni-'ya-su