An Harbe Wani Minista Har Lahira A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20052-an_harbe_wani_minista_har_lahira_a_somaliya
Rahotanni daga Somaliya na cewa an harbe ministan kula da kwadigon jama'a na kasar, Abdullahi Siraji, har lahira a birnin Mogadisho.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
May 04, 2017 05:50 UTC
  • An Harbe Wani Minista Har Lahira  A Somaliya

Rahotanni daga Somaliya na cewa an harbe ministan kula da kwadigon jama'a na kasar, Abdullahi Siraji, har lahira a birnin Mogadisho.

An dai harbe ministan ne a cikin motarsa a kusa da fadar shugaban kasar, saidai har kawo yanzu babu tabas akan yadda lamarin ya auku.

Wasu majiyoyin 'yan sanda dana gwamnati sun shaidawa masu aiko da rahotanni cewa, dakarun tsaron wani jami'in gwamnatin kasar ne suka bude wuta kan motar ministan, amman bisa kuskure. 

Mista Siraji, shi ne minista mafi karancin shekaru a majalisar ministocin kasar, kuma shi ne na farko da aka kashe a cikin irin wannan yanayi a gwamnatin shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed.

Gwamnatin kasar dai ta nuna alhini akan lamarin, inda tuni shugaba Mohamed Abdullahi ya katse ziyara da yake a Habasha.