Tanzaniya : Hadarin Mota Ya kashe Yan Makaranta 29
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20132-tanzaniya_hadarin_mota_ya_kashe_yan_makaranta_29
Rahotanni daga Tanzaniya na cewa yara yan makaranta akalla 29 ne suka rasa rayukansu a yayin wani hadarin mota a arewacin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:04+00:00 )
May 06, 2017 13:09 UTC
  • Tanzaniya : Hadarin Mota Ya kashe Yan Makaranta 29

Rahotanni daga Tanzaniya na cewa yara yan makaranta akalla 29 ne suka rasa rayukansu a yayin wani hadarin mota a arewacin kasar.

Yaran da suka rasu sun hada da mata 17 da kuma maza 12.

Ko baya ga yara akwai jami'an makarantar biyu da kuma drebansu da suka rasu a cikin hadarin kamar yadda darectan makarantar ta Lucky Vincent a Arusha, Innocent Mushi ya sanar. 

Hadarin dai ya auku ne a safiyar wannan Asabar, a yayin da motar safa din ta yan makaranta ta kaucewa hanya ta kuma yi kaca-kaca a cikin kogin Marera dake lardin Karatu.

'Yan makarantar dai na ajin farko 'yan kimanin shekara 12 zuwa 14 na dai na kan hanyarsu ce ta zuwa zana jarabawar share fagen babbar jarawar ta neman zuwa matsakaicin aji.

Tuni dai shugaban kasar John Magufuli  ya isar da ta'aziyarsa ga iyalan yaran da suka rasu., wanda ya danganta da babban rishi ga iyalansu da kuma kasar baki daya.