An Kammala Taron Koli Kan Tattalin Arzikin Afrika
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20126-an_kammala_taron_koli_kan_tattalin_arzikin_afrika
An kammala taron koli na yini uku kan tattalin arzikin Afrika a birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu, inda aka tattauna kan batutuwa da suka shafi samar da ci gaba na bai daya da cinikayya tsakanin kasashen Afrika da kuma amfani da dabarun habaka tattalin arziki na zamani.
(last modified 2018-08-22T07:00:04+00:00 )
May 06, 2017 11:53 UTC
  • Taron Koli tattalin arzikin afrika na 2017
    Taron Koli tattalin arzikin afrika na 2017

An kammala taron koli na yini uku kan tattalin arzikin Afrika a birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu, inda aka tattauna kan batutuwa da suka shafi samar da ci gaba na bai daya da cinikayya tsakanin kasashen Afrika da kuma amfani da dabarun habaka tattalin arziki na zamani.

A jawabinsa yayin rufe taron a jiya Juma'a Mataimakin shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya ce an cimma matsaya kan tinkarar kalubale, sannan an amince a gaggauta kawar da matsalolin da suka hada da wariya da rashin daidaito da kuma rashin aikin yi.

Ya ce yayin taron masu ruwa da tsaki daban-daban sun jaddada cewa, akwai bukatar dora nahiyar kan tafarkin samun dawwamammen ci gaba na bai daya cikin sauri.

Ya ce sakamakon taron zai sauya Afrika daga nahiyar mai buri zuwa wadda ta cimma manufofinta.

Cyril Ramaphosa ya kara da cewa, dole ne a shirya matasa ta yadda za su fuskanci kalubalen da duniya ke fuskanta tare da kokari wajen raya tattalin arziki.