An Fara Taron Tattaunawa Ta Kasa Don Magance Rikicin Kasar Gabon
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20272-an_fara_taron_tattaunawa_ta_kasa_don_magance_rikicin_kasar_gabon
An bude taron tattauna ta kasa a kasar Gabon da nufin kawo karshen rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar to sai dai har ya zuwa yanzu shugaban 'yan adawan kasar Jean Ping yana ci gaba da kaurace wa taron.
(last modified 2018-08-22T07:00:05+00:00 )
May 11, 2017 01:20 UTC
  • An Fara Taron Tattaunawa Ta Kasa Don Magance Rikicin Kasar Gabon

An bude taron tattauna ta kasa a kasar Gabon da nufin kawo karshen rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar to sai dai har ya zuwa yanzu shugaban 'yan adawan kasar Jean Ping yana ci gaba da kaurace wa taron.

Rahotanni daga kasar sun ce kimanin jam'iyyun siyasa 50 da kuma sama da kungiyoyin fararen hula 1000 ne suke halartar wannan taro inda ake tattaunawa batutuwa daban-daban da suka shafi kasar da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance rikicin siyasar da ya kunno kai din.

To sai dai rahotannin sun ce madugun 'yan adawan kasar Mr. Jean Ping wanda aka kayar a zaben shugaban kasar ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin halaltaccen shugaban kasar, ya ci gaba da kaurace wa wannan taron.

A watan Maris din da ya gabata ne shugaban kasar Gabon din Ali Bongo ne ya kaddamar da wannan shirin a kokarin da ake yi na magance rikicin da ya kunno kai bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Augustan da ya gabata da aka sanar da shugaba Bongon a matsayin wanda ya lashe zaben.