Kasashen Afrika Na Cikin ko-ta-kwana Bayan Bullar Ebola A DRC
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20606-kasashen_afrika_na_cikin_ko_ta_kwana_bayan_bullar_ebola_a_drc
Kasashen Afrika da suka hada da Rwanda, Uganda, Ghana, Kenya da Nigeria, sun dauki tsauraran matakai a kan iyakokinsu tun bayan samun rahoton bullar annobar cutar Ebola a Jamhuriyar demokuradiyyar Congo.
(last modified 2018-08-22T07:00:08+00:00 )
May 22, 2017 08:49 UTC
  • Kasashen Afrika Na Cikin ko-ta-kwana Bayan Bullar Ebola A DRC

Kasashen Afrika da suka hada da Rwanda, Uganda, Ghana, Kenya da Nigeria, sun dauki tsauraran matakai a kan iyakokinsu tun bayan samun rahoton bullar annobar cutar Ebola a Jamhuriyar demokuradiyyar Congo.

A kasar Ghana, hukumar kiwon lafiya ta kasar ta bukaci daraktocin shiyya dasu zauna cikin shirin ko-ta-kwana, kuma da zarar sun ga wata alama ta cutar su hanzarta daukar matakan da suka dace ba tare da bata lokaci ba da nufin dakile bazuwar cutar.

A Najeriya ma, ministan lafiya na kasar Isaac Adewole, ya yi irin wannan kiran inda ya shawarci jami'an kiwon lafiya da jama'ar kasar baki daya, dasu gaggauta sanar da duk wata alama da suka samu dake nuna alamun cutar ga jami'an kula da lafiya.

A Rwanda ma, tuni aka kaddamar da shirin yin gwaje-gwaje a kan iyakokin kasar da RD Congon, domin gano masu dauke da cutar.

Su ma a nasu bangare hukumomin kasashen Tanzania da Zambia sun sanar da daukan matakai makamantan hakan a baya bayan nan.