Mabiya Addinai Na Gudanar Da Tattaunawa A Kasar Morocco
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20252-mabiya_addinai_na_gudanar_da_tattaunawa_a_kasar_morocco
An fara gudanar da zaman tattaunawar addinai na kasa da kasa a birnin Hamra na kasar Morocco.
(last modified 2018-08-22T07:00:05+00:00 )
May 10, 2017 14:52 UTC
  • Mabiya Addinai Na Gudanar Da Tattaunawa A Kasar Morocco

An fara gudanar da zaman tattaunawar addinai na kasa da kasa a birnin Hamra na kasar Morocco.

Shafin sadarwa na yanar gizo na Akhbar ya bayar da rahoton cewa, an fara gudanar da wannan zaman tattaunawa ne tare da halartar wakilai daga kasashe daban-daban, kuma za a ci gaba da taron har zuwa gobe Alhamis.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake gudanar da wannan zaman taro a mataki na kasa da kasa, wanda yake mayar da hankalia kan batun zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai na duniya.

Muhammad Al’alawi shi ne wakilin ma’aikatar al’adu ta kasar Morocco wanda ya gabatar da jawabi a wurin, inda ya bayyana cewa kusanto da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai lamari ne mai matukar muhimmanci, musamman a wannan zamani.

Inda ya ce har kulum fahimta a tsakanin al’ummomi da kuma mabanbantan al’adu da addinai na taka gagarumar rawa wajen kyautata zamantakewar jama’a a koina cikin fadin duniya, a kan ya zama wajibi a karfafa irin wannan taro domin samun zaman lafiya da fahimtar juna mai dorewa a duniya.