-
Sojojin Nigeria Sun Kwato Garin Kala Balge Daga Hannun Boko Haram
Mar 24, 2016 23:59Rundunar sojan Nijeriya ta sanar da fatattakan 'yan kungiyar Boko Haram daga garin Kala Balge da ke jihar Borno da kuma kwace ikon garin daga hannun, bugu da kari kan kubutar da mutane kimanin 520 da suke hannun 'yan ta'addan.
-
Helkwatar Sojin Nijeriya Ta Mayar Da Martani Ga Sabon Faifan Bidiyon Shekau
Mar 24, 2016 23:32Helkwatar tsaron Nijeriya ta yi watsi da sabon faifai bidiyon da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar inda ta ce za ta ci gaba da kai hare-haren da take kai wa 'yan kungiyar da nufin ganin bayansu duk kuwa da halin damuwar da Shekau din ya nuna yana ciki a sabon faifan bidiyon.
-
'Yan Sandan Taraba Sun Tabbatar Da Kama Kwamandojin Boko Haram 2
Mar 24, 2016 04:49Rundunar 'yan sandan jihar Taraba a Nijeriya ta tabbatar da kama wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram guda 2 wadanda aka jima ana nemansu inda ta ce tuni ta mika su ga sojoji a jihar.
-
Najeriya: Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kasafin Kudin 2016
Mar 23, 2016 14:44Majalisar dattijan Najeriya ta amince da kasafin kudin da shugaba Buhari ya gabatar mata na shekara ta 2016.
-
Harkar Musulunci Ta Kai Gwamnatin Najeriya kara gaban kotun ICC
Mar 22, 2016 10:06Kwanaki 100 bayan kisan kare dangi da sojoji suka yi a Zariya, Harka Islamiyya ta shigar da gwamnati Tarayya da sojoji kara kotun duniya ICC/CPI da ke birnin Hague bisa kisan sama da mutane 1,000 da sojoji suka yi a Zariya.
-
Shugaba Buhari Ya Gabatar Ga Wasu Shawarwari Na Karfafa Tattalin Arzikin Nijeriya
Mar 22, 2016 06:06Shugaban Muhammadu Buhari na Nijeriya ya gabatar da wasu shawarwari dangane da yadda za a farfado da tattalin arzikin kasar wanda yake cikin mawuyacin hali biyo bayan watandar da mahukuntan kasar da suka shude suka yi da dukiyar kasar da kuma matsalolin tattalin arziki da duniya take fuskanta.
-
An Tabbatar Da Mutuwar Mutane 4 A Zaben Jihar Rivers, Nijeriya
Mar 21, 2016 05:41Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 4 a jihar Rivers biyo bayan rikicin da ya barke a zaben cikin gurbin 'yan majalisun dokokin da aka gudanar a jihar a shekaran jiya Asabar.
-
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Sanar Da Daukan Matakan Magance Rikicin Agatu
Mar 20, 2016 06:02Babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Nijeriya Lt. Janar Yusuf Tukur Buratai ya bayyana cewar rundunar sojin kasar ta dau matakan da suka dace wajen tura sojoji zuwa karamar hukumar Agatu da ke jihar Benue da nufin kawo karshen rikicin da ke gudana tsakanin manoma da fulani makiyaya.
-
MDD ta yi Alawadai da Harin ta'addancin da a kai A Najeria
Mar 17, 2016 23:43Babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya ya yi alawadai da harin ta'addancin da aka kai cikin Masallaci a jihar Borno dake arewa masu gabashin Najeria.
-
Gwamnatin Nigeria Ta Kaddamar Da Shirin Bashin Tallafawa Matasa Na Naira Billion 10
Mar 17, 2016 13:19Gwamnatin tarayyar Nigeria ta kaddamar da shirin tallafawa matasa da bashi na Naira Billion 10.