An Tabbatar Da Mutuwar Mutane 4 A Zaben Jihar Rivers, Nijeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2737-an_tabbatar_da_mutuwar_mutane_4_a_zaben_jihar_rivers_nijeriya
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 4 a jihar Rivers biyo bayan rikicin da ya barke a zaben cikin gurbin 'yan majalisun dokokin da aka gudanar a jihar a shekaran jiya Asabar.
(last modified 2018-08-22T06:58:01+00:00 )
Mar 21, 2016 05:41 UTC
  • An Tabbatar Da Mutuwar Mutane 4 A Zaben Jihar Rivers, Nijeriya

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 4 a jihar Rivers biyo bayan rikicin da ya barke a zaben cikin gurbin 'yan majalisun dokokin da aka gudanar a jihar a shekaran jiya Asabar.

Kafafen watsa labarai sun jiyo Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan sandan Nijeriya Adisa Bolanta yana cewa an tabbatar da mutuwar mutane hudu a yayin rikicin sannan kuma sun kama wasu mutane 22 ciki kuwa har da Sakataren Gwamnatin Jihar da wani babban mai ba wa gwamnan jihar shawara saboda laifin karya dokokin zabe da kuma tada hankulan jama'a.

Shi ma a nasa bangaren kwamandan birget na 2 na rundunar sojin Nijeriya da ke birnin Fatakwal Birgediya Janar Stephenson Olabanji ya tabbatar da cewa rundunar sojin suna tsare da sakataren gwamnati da babban mai ba wa gwamnan shawara wanda ya ce sun kama su ne a kananan hukumomin Gokana da Khana saboda karya dokokin zaben, yana mai watsi da zargin da gwamnatin jihar take yi wa jami'an tsaron na musguna wa manyan jami'an nata inda ya ce babu wani da ya fi karfin doka.

Gwamnan jihar ta Rivers Nyesom Wike ya ce jam'iyyarsu ta PDP ita ce za ta lashe zaben 'yan majalisar da aka gudanar.