Harkar Musulunci Ta Kai Gwamnatin Najeriya kara gaban kotun ICC
Kwanaki 100 bayan kisan kare dangi da sojoji suka yi a Zariya, Harka Islamiyya ta shigar da gwamnati Tarayya da sojoji kara kotun duniya ICC/CPI da ke birnin Hague bisa kisan sama da mutane 1,000 da sojoji suka yi a Zariya.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Musulunci (IHRC) da ke birnin Landon ce ta shigar da karar da hadin gwiwar Harkar Musulunci suna neman a yi adalci kan kasin kiyashin da sojoji suka yi.
A taron manema labarai da Harkar Musulunci ta kira ran Litinin a Kaduna, ta bayyana matukar damuwa a kan rashin bai wa Lauyoyi damar ganin Jagoran Harkar Musulunci, Shekh Ibrahim Zakzaky da gwamanti ta yi.
Harkar Musulunci ta bukaci gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar sakin dukkan 'yan uwan da take tsare da su tsawon watanni uku ba tare da sun aikata laifin komai ba.
Wakilin mu a Abuja Muhammad Sani Abubakar ya tattauna muna da kakakin kungiyar ta harkar musulinci a Najeriya Mal. Ibrahim Musa, kamar yadda zakuji a cikin wannan rahoto