Shugaba Buhari Ya Gabatar Ga Wasu Shawarwari Na Karfafa Tattalin Arzikin Nijeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2779-shugaba_buhari_ya_gabatar_ga_wasu_shawarwari_na_karfafa_tattalin_arzikin_nijeriya
Shugaban Muhammadu Buhari na Nijeriya ya gabatar da wasu shawarwari dangane da yadda za a farfado da tattalin arzikin kasar wanda yake cikin mawuyacin hali biyo bayan watandar da mahukuntan kasar da suka shude suka yi da dukiyar kasar da kuma matsalolin tattalin arziki da duniya take fuskanta.
(last modified 2018-08-22T06:58:01+00:00 )
Mar 22, 2016 06:06 UTC
  • Shugaba Buhari Ya Gabatar Ga Wasu Shawarwari Na Karfafa Tattalin Arzikin Nijeriya

Shugaban Muhammadu Buhari na Nijeriya ya gabatar da wasu shawarwari dangane da yadda za a farfado da tattalin arzikin kasar wanda yake cikin mawuyacin hali biyo bayan watandar da mahukuntan kasar da suka shude suka yi da dukiyar kasar da kuma matsalolin tattalin arziki da duniya take fuskanta.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a wajen taron da majalisar tattalin arzikin kasar ta shirya karkashin jagorancin mataimakinsa Yemi Osinbanjo inda ya kirayi bankuna da su kara taimakawa wajen bayar da rance ga bangaren noma wanda ya ce ita da kiwo su ne manyan hanyoyin arzikin Nijeriyan.

Shugaba Buharin ya bayyana bangarorin noma, wutan lantarki, gidaje da masana'antu a matsayin fagagen da suke bukatar ba da muhimmanci na gaggawa a shirin da ake yi na kyautata yanayin kasar da ya fuskanci koma baya na shekaru aru aru, yana sanar da aniyar gwamnatinsa na kara samar da megawat 10,000 na wutar lantarki a kasar nan da shekaru uku masu zuwa don magance matsalar wutar lantarki da kasar take fuskanta, wanda ake ganin idan aka samar da shi zai taimaka nesa ba kusa ba wajen farfado da masana'antu a kasar.

Majalisar tattalin arzikin kasar (NEC) tana karkashin shugabancin mataimakin shugaban kasar ne Yemi Osinbajo da kuma dukkanin gwamnonin kasar su 36 da kuma wasu ministoci da shugabannin manyan cibiyoyin gwamnati a matsayin membobi.