Rundunar Sojin Nijeriya Ta Sanar Da Daukan Matakan Magance Rikicin Agatu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2695-rundunar_sojin_nijeriya_ta_sanar_da_daukan_matakan_magance_rikicin_agatu
Babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Nijeriya Lt. Janar Yusuf Tukur Buratai ya bayyana cewar rundunar sojin kasar ta dau matakan da suka dace wajen tura sojoji zuwa karamar hukumar Agatu da ke jihar Benue da nufin kawo karshen rikicin da ke gudana tsakanin manoma da fulani makiyaya.
(last modified 2018-08-22T06:58:00+00:00 )
Mar 20, 2016 06:02 UTC
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Sanar Da Daukan Matakan Magance Rikicin Agatu

Babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Nijeriya Lt. Janar Yusuf Tukur Buratai ya bayyana cewar rundunar sojin kasar ta dau matakan da suka dace wajen tura sojoji zuwa karamar hukumar Agatu da ke jihar Benue da nufin kawo karshen rikicin da ke gudana tsakanin manoma da fulani makiyaya.

Janar Buratai ya bayyana hakan ne bayan taron da yayi da wasu jami'an sojin Nijeriyan da suke cibiyar magance rikicin Agatun da ke kusa da garin Otukpo na jihar Benue din don gane wa idanuwansa irin yanayin tsaro da kuma sojojin da aka tura wajen inda ya bayyana tsananin damuwarsa dangane da irin rayuka da dukiyar da aka rasa a yayin rikicin.

Babban hafsan hafsoshin sojin Nijeriyan ya ce babban kwamandan sansanin ya gara masa cewa akwai wasu bata gari da suke satan shanu a yankin don haka sai yayi alkawarin daukan matakan da suka dace wajen kawo karshen hakan da kuma sauran rigingimun da ke faruwa tsakanin manoma da makiyayan.

Rikicin da ya ke ci gaba da faruwa a yankin dai tsakanin manoma da makiyaya yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na mutane da kuma hasarar dukiya mai yawa.