Kame 'yan Da'esh A Kasar Rwanda
Jan 30, 2016 18:04 UTC
Jami'an tsaron kasar Rwanda sun sanar da kame masu mutane masu alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh.
Jami'an tsaron kasar Rwanda sun sanar da kame masu mutane masu alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh.
Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya bada labarin cewa; 'yan sandan kasar ta Rwanda sun kame wasu mutane da su ke bin sawunsu da su ke da alaka da kungiyar Da'esh, sai dai kuma a lokaci guda wasu sun fice daga cikin kasar.
A makon da ya shude ma dai 'yan sandan kasar ta Rwanda sun kashe wani dan kungiyar da Da'esh wanda ya ki amsa kiran da su ke yi masa na mika wuya.
Tags