An Jinkirta Zaben Shugaban Kasa A Congo Kinshasa
Hukumar zabe a jamhuriya Demokuraddiyar Congo ta sanar da jinkirta zaben shugaban kasar na watan Nowamba, wanda hakan zai baiwa shugaban kasar Joseph Kabila ci gaba da mulkin kasar har bayan wa'adin mulkinsa.
A watan Disamba mai zuwa ne wa'adin mulkiin M. Kabila ke kawo karshe, saidai a cewar hukumar zaben kasar saboda rashin kudi da kuma sabunta kundin masu zabe za'a jinkirta zaben.
Koda yake har kawo 'yan adawan kasar basu maida martani ba akan wannan matakin, aman sanin kowa an jima ana fuskantar rikicin siyasa a wannan kasa akan sake tsayawar shugaban kasar takara a zaben mai zuwa.
A nasa bangare mai shiga tsakanin na kungiyar tarrayyar Afrika kan rikicin kasar ta Congo Edem Kodjo, ya kira wani taron 'yan siyasa na kasar domin samun mafita akan jadawalin zaben kasar.