John Kerry Ya Isa Fadar Muhammad Buhari dake Abuja
Bayan da ya kammala ziyarar aiki da ya kai fadar Mai Martaba Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III a Sokoto, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya isa Abuja inda ya soma tattaunawa da shugaban Najeriya Muhammad Buhari
A yayin da yake hira tare da manema labarai a birnin Sokoto, Saktaren Harakokin wajen Amurka John Kerry ya ce dole ne a jinjina wa jami’an tsaron Najeriya, sakamakon kwace muhimman yankuna da kuma ‘yanto dubban mutane daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.
A cewar shi Sojojin Najeriya sun ‘yanto dubban fararen hula, sannan kuma sun kori daruruwan ‘yan Boko Haram tare da kama kwamandojin kungiyar da dama.
A cikin makon da ya gabata sojojin na Najeirya sun ce sun kaddamar da mummunan farmaki wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan Boko Haram masu yawa.
Kerry ya ce Sakamakon taimakon da ta ke samu daga dakarun rundunar hadin-gwiwa na kasashen Amurka, Faransa da kuma Birtaniya, a yau Najeriya ta samu gagarumar nasara wajen rage karfin kungiyar Boko Haram
Sannan ya ce kasashen Kamaru ,Nijar , Chadi da kuma Benin, sun taka gagaruwar rawa domin tabbatar da tsaro akan iyakokin Najeriya, saidai kuma ya yi gargadi ga Sojojin tare da jaddada girman kare hakkin Dan Adam.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama dai sun zargi Sojojin Najeriya da wuce gona da iri wajen kisan fararen hula da sunan farautar ‘Yan Boko Haram.
Ziyarar ta John Kerry ta biyo bayan wacce ya kai kasar Kenya tun daga shekaranjiya kafin daga bisani ya isa zuwa tarayyar Najeriya