Yajin aikin gama gari a Jumhoriyar Demokradiyar Kwango
'Yan Adawar Shugaban kasar Demokaradiyar Kwango sun fara yajin aiki na gama gari
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa A yau Talata magoya bayan jami'iyun adawar Shugaba Joseph Kabila na Jumhoriyar Demokaradiyar Kwango sun yi tsuntsurundo a gaban babbar cibiyar Jam'iyar Adawa a Kinshasa babban birnin Kasar, domin tarwatsa su jami'an 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye.
Rahoton ya ce mafi yawan shagudan dake birnin kinshasa sun kasance a rufe kuma idan ka zagaya tutunan birnin za ka ga kamar an share Mutane saboda mafi yawa daga cikin su sun yi zamansu a gidajen su.
A yau Tatata ce Gwamnatin kasar Kwangon ta kudiri wani zama na tsara jadawali zaben shugaban kasar da ya kamata aka gudanar da shi a watan Nuwamba na wannan shekara, to saidai saboda rashin shiri daga Hukumar Zaben kasar, an dage zaben har zuwa shekara mai kamawa.
Manufar wannan yajin aiki da kuma zanga-zangar hana zaman da Gwamnati ta kudiri yi a wannan talata saboda a cewa 'yan adawar wani shiri ne na baiwa Shugaba Joseph Kabila damar ci gaba da zama a kan karagar milki.