Kasashen Sudan Biyu Sun Amince A Bude Kan Iyakokinsu
Aug 24, 2016 07:47 UTC
Jami'an gwamnatocin Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun cimma yarjejeniyar Bude kan iyakokinsu Biyu
Jami'an gwamnatocin Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun cimma yarjejeniyar Bude kan iyakokinsu biyu.
Cimma yarjejeniyar a tsakanin kasashen biyu dai ya zo ne bayan ganawar da aka yi a tsakanin mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu, Taban Dang Gai, da shugaba Umar Hassan al-Bashir a jiya litinin a birnin Khartom.
Bugu da kari, bangarorin biyu sun tattauna akan batutuwan da su ka shafi tsaro da kuma batun man fetur.
A gefe daya, kasar Sudan ta baiwa Sudan ta kudu tabbacin cewa ba za ta bada dama ga 'yan atwaye su sami matsugunni a cikin kasar ba.
Tags