An Tsaurara Matakan Tsaro A Kan iyakokin Kenya Da Somaliya
Mahukunta a kasar Kenya sun sanar da daukar kwararan matakai a kan iyakokin kasar da kuma kasar Somalia, sakamakon karuwar barazanar tsaro a yankin.
Kmafanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoton cewa, babban kwamandan rundunar hadin gwiwa da ke yaki da ayyukan ta'addanci a yankunan arewa maso gabashin kasar Kenya Mohammad saleh ya bayyana cewa, sun kara yawan jami'an tsaro a yankin, sakamakon barazanar da ake fuskanta daga mayakan Al-shabab da suke shigowa cikin kasar daga Somalia.
Ya ce a cikin Afirilun da ya gabata, mayakan Al-shabab sun kaddamar da hari kan manyan na'urorin kamafanin sadarwa na kasar Kenya Safaricom, daga bisani kuma an samu wasu bayanan sirri da suke tabbatar da cewa mayakan kungiyar na shirin fara tarwatsa manyan butatai na ruwa a kasar, wanda hakan ya sa ala tilas a kara tsaurara matakan tsaro a yankunan da ke iyaka da kasar ta Somalia.