Shugaban Gabon Ya Bayyana Kansa A Matsayin Dan Takara Mafi Dacewa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10132-shugaban_gabon_ya_bayyana_kansa_a_matsayin_dan_takara_mafi_dacewa
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya bayyana kansa a matsayin dantakarar shugabancin mafi dacewa da duk wani canji da ake bukata a kasar a halin yanzu.
(last modified 2018-08-22T06:58:49+00:00 )
Aug 25, 2016 01:17 UTC
  • Shugaban Gabon Ya Bayyana Kansa A Matsayin Dan Takara Mafi Dacewa

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya bayyana kansa a matsayin dantakarar shugabancin mafi dacewa da duk wani canji da ake bukata a kasar a halin yanzu.

A wata zantawa da ta hada shi da tashar talabijin ta France 24 a daren jiya, Ali Bongo ya bayyana cewa, kasar Gabon tana cikin wani yanayi da ke bukatar a yi dogon nazari kan makomarta, musamman ta fuskar tattalin arziki, inda a cewarsa yana da masaniya kan kan kasar da kuma abin da take bukata.

A ranar Asabar mai zuwa ce dai za a gudanar da zaben shuagabn kasa a kasar ta Gabon, inda Ali Bongo yake fuskantar matsaloli masu tarin yawa, da suka hada da zarginsa da rashin kasancewa cikakken dan kasa.