Yarjejjeniyar Sudan da Sudan ta Kudu kan sake buda iyakokin kasashen biyu
Kasar Sudan da Sudan ta kudu sun cimma matsaya a kan sake buda iyakokin kasashen biyu.
A ranar talatar da ta gabata, wata tawagar kasar Sudan ta kudu bisa Jagorancin Mataimakin shugaban kasar na farko Taban Deng Gai ta kai ziyara zuwa kasar Sudan.A yayin ganawarta da Shugaba Umar Albashir,magabatan kasashen biyu sun tattauna kan batutuwa da dama kama daga batun tsaro, alakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma yarjejjeniyar da aka cimma kan batun safarar Man fetur din sudan ta kudun dake bi ta kasar sudan din zuwa kasuwanin Duniya.
Bisa yarjejjeniyar da aka cimma ana sa ran nan da makuni uku masu zuwa za a bude iyakokin kasashen biyu. magabatan Sudan ta kudu sun tabbatarwa takwarorin nasu na sudan da cewa ba za su bar 'yan tawayen Sudan ba su ci gaba da aiyukansu a cikin kasar Sudan ta kudun,.a nasu bangare magabatan Sudan din sun yi alkawarin taimakawa 'yan gudun hijrar Sudan ta kudun mabuka da abinci wadanda suke rayuwa a cikin kasar Sudan din, ana fatan wannan ziyara ta zamanto wani sanadi da zai sanya yanayin da 'yan gudun hijrar Sudan ta kudun suke ciki da dan gyaru.
A watan Maris din da ya gabata, Gwamnatin sudan ta sanar da cewa za ta yi mu'amala da 'yan kasar sudan ta kudun dake cikin kasar kamar sauren 'yan kasashen waje, inda ta ce wajibi ne ga dukkanin 'yan kasar Sudan ta Kudun dake zaune a cikin kasar su tanadi takardun zaman kasa kamar yadda sauren 'yan kasashen waje suka tanada, kuma kafin shiga cikin kasar wajibi ne su dauki biza.
Bisa alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, kimanin 'yan kasar Sudan ta Kudu dubu 198 da 600 ne suka yi hijra zuwa Sudan din sanadiyar rikicin watan Decemba na shekarar 2013.
A halin da ake ciki, mafi yawan 'yan gudun hijrar Sudan ta kudun na zaune ne a sansanin 'yan hijrar Majalisar dinkin Duniya guda bakwai dake cikin yankunan Nail Abyad, Darfur ta gabas, da babbar birnin kasar watau Khartum.
Ko baya ga batun 'yan gudun hijrar Magabatan Sudan ta kudun su tabo batun yarjejjeniyar da kasashen suka cimma na shekarar 2012 dangane da safarar Man fetur din kasar zuwa kasuwanin Duniya da zai kare a watan Nuwamba na wannan shekara ta 2016, Ministocin Man na kasashen biyu sun tattaunawa a kan kula sabuwar yarjejjeniya kuma ana sa ran nan da wata mai zuwa Ministocin kasashen biyu za su sake wani zama domin ci gaba da tattaunawa kan wannan batu.
A halin da ake ciki , kasar Sudan ta kudun na fitar da ganga dubu 150 kacal a ko wata Rana, idan kuma aka kwatamta da Lokacin da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 2011, adadin ya ragu da sama da shi 50% inda a wancan lokaci take fitar da ganga dubu 350 a ko wata rana.