Kenya: Fiye Da 'Yan gudun Hijirar Somaliya Dubu 20 Sun Koma Gida
Majialisar Dinkin Duniya ta ce; Fiye da "yan gudun hijirar kasar Somaliya 24,000 a Kenya sun koma gida.
Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin, ya nakalto majiyar hukuma mai kula da 'yan gudn hijira ta majalisar dinkin duniya tana cewa; Daga lokacin da aka cimma yarjejeniya tsakanin kenya da Somaliya da kuma wakilan majalisar dinkin duniya, a 2014 zuwa yanzu, 'yan gudun hijirar Somaliya dubu 24 ne su ka bar kasar Kenya zuwa gida.
Wakilin Hukumar 'yan gudun hijirar majalisar dinkin duniyar ya isa sansanin 'yan gudun hijira na Dedav da ke kasar Kanya da kuma Somaliya a jiya laraba, domin samun battacin cewa 'yan gudun hijirar sun koma ne bisa radin kansu, kuma cikin mutuntawa.
Kasar Kenya ta yanke shawarar rufe sansanin 'yan gudun hijira na Dedav ne bisa dalilai na tsaro. Da akwai fiye da 'yan kasar Somaliya 300,000 a cikin sansanin 'yan gudun hijirar.