Yajin Aikin Kwararrun Likitoci Na Kwana Biyar A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10153-yajin_aikin_kwararrun_likitoci_na_kwana_biyar_a_nijar
Likitocin Jamhuriyar Nijar Suna Yajin Aiki
(last modified 2018-08-22T06:58:49+00:00 )
Aug 25, 2016 07:38 UTC
  • Yajin Aikin Kwararrun Likitoci Na Kwana Biyar A Nijar

Likitocin Jamhuriyar Nijar Suna Yajin Aiki

Cibiyar Watsa Labaru Ta "Africa Times" daga birnin Yamai a Nijar ta ambato cewa; Kwararru liktoci sun shiga yajin aiki na kwana biyar daga jiya laraba.

Majiyar ta ce; yajin aikin ya haddasa tsaiko wajen tafiyar da ayyuka a manyan asibitoci biyu mallakin gwmanati  da kuma wuraren bada magani a birnin na Yamai.

Shekaru biyu kenan ajere da kungiyar likitoci a jamhuriyar ta Nijar ta ke takkaddama da gwamnati akan batun karin albashi da kuma na karin ilimi.