Jawabin Shugaban Kasar Gabon A Jajiberin Zabe
Aug 26, 2016 07:17 UTC
Ali Bango Ya ce; Shi ne zai sake lashe zabe
Shugaban Kasar Gabon Ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi dacewa da kawo sauyi acikin kasar.
A wata hira da tashar taelbijin din Farace 24 ta yi da shi, Ali Bongo ya ce; A zaben da za a yi na ranar 27 ga watan Augusta al'ummar kasar za su kada masa kuri'a ne.
Har ila yau, Bongo ya ambaci yadda mahaifinsa da kuma shi su ka mulkin kasar na tsawon rabin karni, sannan ya kara da cewa; al'ummar suna da cikakkiyar masaniya akan ayyukan da su ka yi, don haka shi za su zaba.
A shekarar 2009 ne Ali Bango ya gaji mahaifinsa Umar Bango wanda ya mulki kasar Gabon na tsawon shekaru 41.
Tags