Shugaba Mugabe ya galgadi Masu Adawa da shi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10204-shugaba_mugabe_ya_galgadi_masu_adawa_da_shi
Shugaban Kasar Zimbabwe ya galgadi masu zanga-zangar adawa da Gwamnatin sa
(last modified 2018-08-22T06:58:50+00:00 )
Aug 27, 2016 01:04 UTC
  • Shugaba Mugabe ya galgadi Masu Adawa da shi

Shugaban Kasar Zimbabwe ya galgadi masu zanga-zangar adawa da Gwamnatin sa

Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya habarta cewa A jiya Juma'a Shugaban Kasar Zimbabwe ya ja kunan masu adawa da Gwamnatin sa, inda ya ce zanga zangar da su keyi babu wani tasiri da za ta yi.

Shugaba Mugabet ya ce 'yan adawar na kona tayoyi a kan tituna domin kwace milki daga hanunsa, a tunanin su juyin juya halin da ya faru a wasu kasashen larabawa na iya faruwa a kasar Zimbabwe.

Jim kadan bayan jawabin na Shugaba Mugabet , Jami'an 'yan sanda sun yi dirar mikiya a kan masu Zanga-zangar inda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa su,

har ila yau 'Yan sandan sun harba hayaki mai sa hawaye a kan shugabannin 'yan adawar kasar Morgan Tsvangirai da tsohon mataimakin shugaban kasar Joice Mujuru yayin da gangamin zanga-zangar adawa da shugaban kasar Robert Mugabe ta rikide zuwa tarzoma.

A 'yan watannin baya bayan nan dai jami'an tsaron sun zafafa dirar mikiya sakamakon karuwar zanga-zangar adawa da shugaba Mugabe da Jam'iyyarsa ta ZANU-PF yayin da jama'a suke nuna bacin rai kan tabarbarewar tattalin arziki da rashin ayyukan yi da kasar ke fama da su, tare kuma da neman Gwamnati ta gudanar da wasu gyare gyrare a tsarin zabe mai zuwa na 2018.