An cabke wanda ya jagoranci 'yan wasan kasar Kenya zuwa Olanpiya
Majiyar tsaron kenya ta sanar da kame wanda ya jagoranci 'yan wasan kasar zuwa Olanpiya
Kamfanin dillancin labaran tashar Telbijin da radio na kasar Iran ya nakalto wata majiyar 'yan sandar kasar Kenya da ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce bisa bukatar Gwamnatin kasar da kuma bincike kan wasu magudan kudade da suka bace a bangaren kwamitin tare da gyara kuraran da aka yi na tura 'yan wasan da suka dace a wasan Olanpiya da ya gudana a garin Rio de Janeiro na kasar Brazil, an cabke Francis Paul shugaban kwamitin da ya jagoranci 'yan wasan kasar zuwa wassanin Olanpiya.
Majiyar ta ce a halin da ake ciki Mista Paul na daure a gidan kaso, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin zagulo sauren magabatan kwamitin.
An gudanar da wasan Olanpiyan ne daga ranar 6 zuwa ga ranar 21 ga wannan wata na Agusta da muke ciki, inda 'yan wasa dubu 10 da 444 daga kasashe 206 a kuma bangaren wassani 28 suka halarci wasanin a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.