Ci Gaba Da Dambaruwar Siyasar Kasar Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10210-ci_gaba_da_dambaruwar_siyasar_kasar_sudan
Dambaruwar siyasa tana ci gaba da daukan sabon salo a kasar Sudan sakamakon rashin cimma wata kwakkwarar matsaya a zaman taron kasa da ake gudanarwa da nufin samar da hanyar warware rikici da tashe -tashen hankula da suke ci gaba da addabar kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:50+00:00 )
Aug 27, 2016 01:19 UTC
  • Ci Gaba Da Dambaruwar Siyasar Kasar Sudan

Dambaruwar siyasa tana ci gaba da daukan sabon salo a kasar Sudan sakamakon rashin cimma wata kwakkwarar matsaya a zaman taron kasa da ake gudanarwa da nufin samar da hanyar warware rikici da tashe -tashen hankula da suke ci gaba da addabar kasar.

Manufar gwamnatin Sudan ta shirya zaman taron  kasa ita ce samar da hanyar warware dambaruwar siyasar kasar ta hanyar lumana musamman rikici da tashe -tashen hankula da sunan tawaye a yankunan da suke lardunan Darfur da Blue Nile da kuma Kurdufon da Kudu amma tun fara gudanar da zaman taron har yanzu babu wata kwakkwarar matsaya da aka cimma a tsakanin gwamnati da 'yan adawar kasar.

Har ila yau zaman tattaunawan neman yin sulhu da aka gudanar tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyoyin 'yan tawayen kasar karkashin sa-idon kungiyar tarayyar Afrika a makon da ya gabata a Cibiyar kungiyar tarayyar Afrika da ke birnin Adis Ababa na kasar Habasha babu wata matsaya da aka cimma, inda mahukuntan Sudan suke zargin kungiyoyin 'yan tawayen kasar da rashin mutunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta, yayin da kungiyoyin 'yan tawayen kasar suke zargin gwamnatin Sudan da cewa bata gaske take yi ba kan batun neman warware matsalolin da suke addabar kasar musamman dagewarta kan rashin mutunta mahangar 'yan tawayen kasar.

A gefe guda kuma Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Afrika sun yi kakkausar suka kan rashin cimma matsaya a zaman tattaunawan sulhu tsakanin gwamnatin Sudan da 'yan tawayen kasar a makon da ya gabata. A halin yanzu haka dai ana ci gaba da samun bullar dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da gungun 'yan tawayen kungiyar Sudan Liberation Movement da na Justice and Equality Movement a yankin Darfur da ke yammacin kasar, kamar yadda a yankunan lardunan Kordofan ta Kudu da Blue Nile gumurzu tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da 'yan tawayen kungiyar Sudan People's Liberation Movement -North {SPLM-North} a takaice ke ci gaba da daukan sabon salo.

Kungiyoyin 'yan tawayen Sudan da suka hada da na yankin Darfur da kuma lardunan Kordufan ta Kudu da Blue Nile suna zargin gwamnatin Umar Albashir ne da rashin kula da matsalolin rayuwa da na zamantakewa gami da siyasa a yankunansu amma maimakon gwamnati ta dauki matakin warware matsalolin sai ta gwammace yin amfani da karfi kan al'ummun yankunan saboda kasancewar 'yan tsirarun kabilu a kasar.

Shugaba Umar Hasan Albashir ya dare kan karagar shugabacin kasar Sudan ne tun bayan juyin mulkin da ya gudanar a ranar 30 ga watan Yunin shekara ta 1989, sannan ya rikide zuwa farin hula tare da tsayawa takarar shugabancin kasar kuma ya lashe zabe a shekara ta 1993, inda har zuwa yanzu yake jan ragamar shugabancin kasar tsawon shekaru 27, Umar Hasan Albashir ya yi da'awar cewa a bayan wa'adin mulkinsa a shekara ta 2020 zai yi murabus daga fagen siyasar kasar lamarin da wasu masharhanta ke ganin kokari kawai na rage kaifin suka da adawa kansa.