Bude Cibiyar Sulhu A Tsakanin Addinai A Nigeria
An kaddamar da wata sabuwar cibiya ta yin sulhu da kawo zaman lafiya a tsakanin musulmi da kiristoci a garin Kaduna na Najeriya.
Shafin yada labarai na yanar gizo na Christian Daily ya habarta cewa, musulmi da kiristoci sun gudanar da zama a birnin Kaduna, kuma babbar manufar wannan cibiya dai ita ce yada fahimtar juna da kauna a tsakanin jama’ar Najeriya, da kuma kauce wa duk wani abin da zai kawo tashin hankali a tsakanin jama’a, musamman ma dai mabiya wadannan manyan addnai na kasar.
Fiye da mutane dubu 20 ne dai ake cewa sun mutu sakamakon tashe-tashen hankula a Najeriya a cikin shekarun baya-bayan nan, duk kuwa da cewa mahuknta ba su tabbatar da wadannan alkalumma a hukumance ba.
Olaw Fiske babban sakataren majalisar majam’ion mabiya addinin mirista na duniya dangane da wannan batu ya bayyana cewa; hakika kafa wannan cibiya a Kaduna yana da matukar muhimmanci, kuma zai mayar da wannan birnin babbar cibiyar sulhu da zaman lafiya a kasar baki daya.