A Yau Ne Al'ummar Kasar Gabon Ke Kada Kuri'ar Zaben Shugaban Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10221-a_yau_ne_al'ummar_kasar_gabon_ke_kada_kuri'ar_zaben_shugaban_kasa
Al'ummar kasar Gabon na gudanar da zaben shugaban kasa a yau domin zaben daya daga cikin 'yan takara sha hudu da suke karawa da juna domin neman kujerar shugabancin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:50+00:00 )
Aug 27, 2016 06:30 UTC
  • A Yau Ne Al'ummar Kasar Gabon Ke Kada Kuri'ar Zaben Shugaban Kasa

Al'ummar kasar Gabon na gudanar da zaben shugaban kasa a yau domin zaben daya daga cikin 'yan takara sha hudu da suke karawa da juna domin neman kujerar shugabancin kasar.

Tashar talabijin ta France 24 ta bayar da rahoton cewa, tun da safiyar yau ne jama'a suka fara isa runfunan zabe domin kada kuri'unsu, kuma zaben yana gudana lami lafiya.

Tun kafin wannan lokacin dai kungiyar tarayyar Afirka da kuma kungiyar tarayyar turai sun kirayi dukkanin bangarorin da ke karawa da juna na jam'iyya mai mulki da sauran jam'iyyun adawa da su tabbatar da cewa sun guji duk wani abin da ka iya kawo tashin hankali a zaben.

Shugaba Ali Bogo dan takarar jam'iyya mai mulki, na fuskantar babbar hamayya daga dan takarar adawa kuma tsohon shugaban kungiyar tarayyar Afirka Jean Ping.

Idan aka kasa samun daya daga cikin 'yan talarar hudu da ya lashe fiye da kashi hamsin cikin dari, za a je zabe zagaye na biyu.