Tsagerun "Avengers" Sun Sanar Da Dakatar Da Hare-Hare A Niger Delta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10333-tsagerun_avengers_sun_sanar_da_dakatar_da_hare_hare_a_niger_delta
Kungiyar tsagerar yankin Niger Delta da take kiran kanta da Avengers ta sanar da dakatar da kai hare-haren da take yi wa bututun man fetur a yankin Niger Delta na Nijeriya a daidai lokacin da sojojin kasar suka sanar da fara kaddamar da wasu hare-hare kan tsagerun.
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Aug 30, 2016 01:25 UTC
  • Tsagerun

Kungiyar tsagerar yankin Niger Delta da take kiran kanta da Avengers ta sanar da dakatar da kai hare-haren da take yi wa bututun man fetur a yankin Niger Delta na Nijeriya a daidai lokacin da sojojin kasar suka sanar da fara kaddamar da wasu hare-hare kan tsagerun.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar tsagerun Avengers din sun sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da suka buga a shafinsu na Internet inda suka ce sun saurari kiran tattaunawa da gwamnatin ta gabatar don haka sun dakatar da hare-haren na su, sai dai kuma sun ce suna fatan ganin gwamnatin ta yi abin da ya dace da ita.

Tsagaita wutar dai ta zo ne mako guda bayan da tsagerun suka sanar da cewa suna shirye su tattauna da gwamnatin tarayyar Nigeria bayan sanarwar da gwamnatin ta yi na cewa ita ma a shirye take ta tattauna da tsagerun don dakatar da hare-haren da suke kai wa bututun mai na kasar lamarin da ya rage irin man da Nijeriyar take fitarwa a kowace rana da kimanin ganga dubu 700 abin da ya ke ci gaba da janyo gibi cikin kudaden shigar da kasar take samu.

A ranar Asabar din da ta gabata ce rundunar sojin Nijeriyan ta sanar da cewa ta kaddamar da wasu sabbin hare-haren kan tsagerun Niger Deltan inda ta kashe mutane biyar da kuma kama wasu 23, a kokarinta na kawo karshen ayyukan zaton kasa ga tattalin arzikin kasar da suke yi.