Ci gaba Da Fada A Kasar Sudan Ta Kudu Bayan Sulhu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1036-ci_gaba_da_fada_a_kasar_sudan_ta_kudu_bayan_sulhu
Mjalisar DInkin Duniya Ta Zargi Bangarorin gwamnati da 'Yan Hamayyar Sudan Ta Kudu Da Ci gaba da Kashe Mutane
(last modified 2018-08-22T06:57:50+00:00 )
Feb 20, 2016 09:46 UTC
  • Ci gaba Da Fada A Kasar Sudan Ta Kudu Bayan Sulhu

Mjalisar DInkin Duniya Ta Zargi Bangarorin gwamnati da 'Yan Hamayyar Sudan Ta Kudu Da Ci gaba da Kashe Mutane

Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato majiyar majalisar dinkin duniyar na cewa; Tare da cewa bangarorin gwamnati da kuma 'yan tawaye sun cimma yarjejeniya amma duk da haka suna ci gaba da kashe mutane da sace wasu sannan da rusa dukiyoyi.

Shekaru biyu kasar ta Sudan ta Kudu tana fama da yakin basasa, tsakanin shugaba Silva Kiir da kuma mataimakinsa Reik Machar.

A makon da ya shude ne dai bangarorin biyu su ka cimma yarjejeniyar sulhu, wacce ta kunshi maida Reik Machar kan mukaminsa na mataimakin shugaban kasa.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Bon Ki Moon yana shirin kai ziyara ne zuwa kasar ta Sudan ta kudu a ranar alhamis mai zuwa domin ganawa da shugaba Silva Kir.