Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Bukatar Samun Zaman Lafiya A Kasar Gabon
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10360-majalisar_dinkin_duniya_ta_jaddada_bukatar_samun_zaman_lafiya_a_kasar_gabon
Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada bukatar nisantar duk wani abin da zai janyo tashe-tashen hankula sakamakon sabanin siyasa a kasar Gabon.
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Aug 30, 2016 06:30 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Bukatar Samun Zaman Lafiya A Kasar Gabon

Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada bukatar nisantar duk wani abin da zai janyo tashe-tashen hankula sakamakon sabanin siyasa a kasar Gabon.

A bayanin da ya fitar a yau Talata Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya yi kira ga dukkanin jam'iyyun siyasa a kasar Gabon da su dauki matakin mutunta sakamakon zaben shugabancin kasar da Hukumar zabe zata sanar tare da nisantar duk wani abin da zai janyo bullar tashe-tashen hankula a kasar.

Stephane Dujarric ya kara da cewa: Mutunta sakamakon zaben shugabancin kasa a Gabon ita ce kawai zata kai ga zaman lafiya da mutunta tsarin dimokaradiyya a kasar, sannan duk mai korafi kan sakamakon zaben ya bi hanyar doka domin neman hakkinsa.

Tuni dai Jean Ping daga cikin 'yan adawar kasar ta Gabon ya shelanta nasararsa a zaben shugabancin kasar, yayin da magoya bayan shugaban kasar ALi Bango suke ci gaba da murnar lashe zaben da ake sa- ran sanar da sakamakonsa a yau Talata.