Ana Dakon Sakamakon Zabe A Gabon
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10369-ana_dakon_sakamakon_zabe_a_gabon
Al’ummar kasar Gabon na ci gaba da dakon sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar, a ranar asabar da ta gabata, a daidai lokacin da 'yan adawa da jam'iyya mai mulki ko wanne ke ikirarin shi ya lashe zaben.
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Aug 30, 2016 13:46 UTC
  • Ana Dakon Sakamakon Zabe A Gabon

Al’ummar kasar Gabon na ci gaba da dakon sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar, a ranar asabar da ta gabata, a daidai lokacin da 'yan adawa da jam'iyya mai mulki ko wanne ke ikirarin shi ya lashe zaben.

A yayin da dan takarar adawa Jean Ping ke bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shi ma shugaba mai-ci Ali Bongo Ondumba na  ikirarin nasara.

Hakan yasa shugaban hukumar zaben kasar ta Gabon Rene Agbo Eta, ya bukaci jama’a su kwantar da hankulansu, domin kuwa za'a fitar da sakamakon nan bada dadewa ba.

kafin hakan dama wakilan tarayyar turai masu sa’ido kan zaben kasar ta Gabon sun bayyana fargaba bisa yadda za’a bayyana sahihin sakamakon zaben shugaban kasar. 

Masu sa ido daga kungiyar ta EU sun bayyana cewar zaben ya gaza mizanin da ake bukata.

Shugabar tawagar mai mutane 73 da suka sa ido kan zaben Mariya Gabriel, Yar Majalisar kasar Bulgaria ta bayyana damuwa kan yadda hukumar zaben kasar ta gudanar da ayyukan ta da kuma yadda ta boye bayanai na adadin masu kada kuri’u da yawan mazabu.

Mariya Gariel tace mako guda kafin gudanar da zaben rabin mutanen da suka yi rajista ne kawai suka samu katin zaben su.