Ziyarar Shugaban Kasar Kenya a Sudan ta Kudu.
Shugaban Kasar Kenya ya kama hanyar kasar Sudan ta kudu da nufin ganawa da magabatan kasar dangane tattauanwar sulhu tsakanin bangarorin dake fada da juna a kasar
Kamfanin dillancin Labaran Isna ya habarta cewa a wannan Laraba ake sa ran Shugaba Uhuru kinyata na kasar Kenya zai gana da Shugaba Salva keir na Sudan ta kudu da nufin shiga tsakani kan rikicin ya sake kunno kai a Sudan ta kudu.
Bisa sanarwa da birnin Nairobi ya fitar, shugabanin kasashen za su tattauna kan yarjejjeniyar sulhun da aka cimma a karshen shekarar da ta gabata bisa shiga tsakani na kungiyar Tarayar Afirka a birnin Abis Ababa na kasar Habasha dake a matsayin hedkotar kungiyar tarayar Afirkan.
Ana sa ran bayan tattaunawar, magabatan biyu za su halarci taron manema labarai domin bayanawa Duniya sakamakon tattauanwar.