Kotun koli ta yi watsi da Bukatar Sakin Shekh Zakzaky A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10387-kotun_koli_ta_yi_watsi_da_bukatar_sakin_shekh_zakzaky_a_najeriya
Kotun Koli a Najeriya ta yi watsi da bukatar sakin Shugaban 'yan uwa musulmi mabiya mazhabar Shi'a Shek Ibrahim Elzakzaky daga lauyoyinsa
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Aug 31, 2016 03:31 UTC
  • Kotun koli ta yi watsi da Bukatar Sakin Shekh Zakzaky A Najeriya

Kotun Koli a Najeriya ta yi watsi da bukatar sakin Shugaban 'yan uwa musulmi mabiya mazhabar Shi'a Shek Ibrahim Elzakzaky daga lauyoyinsa

Kotun ta bayyana dalilanta a kan cewa ba ta samu rahoto dangane da shara'ar da ta gabata a kan lokaci ba kuma babu wani jami'in dan sanda da ya halarci kotun domin bada ba'asi kan abinda ya wakana don haka ba za ta iya bada balin ba kamar yadda wakilan Jagoran 'yan uwa musulmin suka bukata.

A  Makun da ya gabata 'yan uwa musulmi mabiya mazhabar shi'a almajiran Shekh Ibrahim Elzakzaky sun gudanar da gagarumar zanga-zanga wacce ita irinta ta farko a garin Kanuda domin neman a gaggauta sakin Jagoran na su tare da mabiyan sa wadanda suke tsare a hanun jami'an tsaro.a nasu bangare jami'an tsaron  kasar sun tsananta kai sumame a Husainiya bakiyatull.. dake birnin Zariya.

Kungiyyoyin kare hakin bil-adama sun yi ta galgadin yanayin da kuma halin da Jagoran 'yan uwa musulmi shekh Ibrahim Elzakzaky ke ciki a gurin da yake tsare inda suka bukaci da a gaggauta  kaishi wajen kwararun likitoci domin yi masa magani.

Bisa sanarwar da Kwararu na Mazhabar Shi'a ta Duniya suka yi, manufar harin da Sojojin Najeriya suka yi a kan mabiya mazhabar Shi'a tare kuma da kame Jagoransu, shi ne rusa hakarakar musulinci gaba daya a kasar.

A ranar 13 ga watan Decembar shekarar da ta gabata ce Sojojin Najeriya cikin manyan tankokin yaki suka hari a Husainiya Bakiyatul...dake birnin Zariya inda suka kashe dariruwan Musulmi tare kuma da jikkata wasu dariruwa na daban gami da kame Jagoran 'yan uwan bayan da suka yi masa halbi kimani uku zuwa hudu a jikinsa