Zaben Gabon Ya Bar Baya Da Kura
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10417-zaben_gabon_ya_bar_baya_da_kura
Rahotanni daga Gabon na cewa ana cikin halin dar-dar a washe garin sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da Ali Bongo Ondimba ya sake lashewa.
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Sep 01, 2016 03:12 UTC
  • Zaben Gabon Ya Bar Baya Da Kura

Rahotanni daga Gabon na cewa ana cikin halin dar-dar a washe garin sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da Ali Bongo Ondimba ya sake lashewa.

A Jiya ne dai hukumar zaben kasar ta sanar da shugaba Ali Bango mai barin gado a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar, da aka gudanar a ranar Asabar bayan da ya doke abokin hamayarsa Jean Ping, wanda kuma ya yi watsi da sakamakon.

Bayan hakan ne dai rikici ya barke musamman a Libreville babban birnin kasar, inda magoya bayan Jean Ping suka bazu cikin tituna don kalubalantar sakamakon zaben, lamarin da ya kai har ga kona majalisar dokokin kasar.

'Yan sanda dai sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa magoya bayan Jean Ping.

Ana cikin wannan ne kuma jami'an tsaro suka yi dirar mikiya a babban offishin jam'iyyar 'yan adawa ta kasar dake birnin na Libreville, inda wasu rahotanni ke cewa sunyi amfani da jirgi mai saukar ungula inda suka bude wuta kan ofishin lamarin da yayi sanadin jikatar mutane 19 ciki har da masu munanen raunuka, kamar yadda shi ma jagoran 'yan adawa na kasar Jean Ping ya tabbatarwa da kanfanin dillancin labarai na AFP.

Hukumar zaben kasar CENAP ta dai bayyana shugaba Ali Bango da cewa shi ne ya lashe zaben da kashi 49,85% a gaban abokin takararsa Jean Ping da ya samu kashi 48,16%, amma ‘yan adawa suka bukaci da a sake gudanar da kidayar kuri’un a wani yanki na kasar, musamman mahaifar 'Ali Bongo, ta Asali, inda yawan wadanda suka halarci zaben a yankin ya kai 99,98%.

A nata bangare kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci hukumar zaben kasar da ta bayyana filla-filla sakamakon ko wace runfar zabe, tare da yin kiran ga bangarorin biyu da su kai zuciya nesa.