Tabbatar da sakamakon zaben Gabon
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10456-tabbatar_da_sakamakon_zaben_gabon
Bisa Sakamakon zaben da Hukumar zaben kasar ta sanar a hukumanci Shugaban kasar Gabon mai ci Ali Bongo ne ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata.
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Sep 02, 2016 01:06 UTC
  • Tabbatar da sakamakon zaben Gabon

Bisa Sakamakon zaben da Hukumar zaben kasar ta sanar a hukumanci Shugaban kasar Gabon mai ci Ali Bongo ne ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata.

Ministan cikin gida na kasar Gabon, ya bayyana shugaban kasar, Ali Bongo a matsayin  wanda ya samu nasarar zaben shugabancin kasar, da tazaran kuri'u kimanin dubu shida ne Ali Bongo mai shekaru 57 ya samu damar darewa kan kujerar shugabancin kasar karo na biyu inda ya samu kashi 49.80 cikin 100 na kuri'un 'yan kasar yayin da abokin takaransa Jean Ping ya samu kashi 48.23 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.To sai dai tuni Jean Ping ya yi watsi da sakamakon wannan zabe, wanda hakan ya tinzira magoya bayansa suka soma zanga-zangar a ofishin hukumar zaben kasar.

A yayin bayyana sakamakon zaben wakilan bangaren Adawa ya fice daga zauren hukumar zaben inda suka bukaci da a wallafa sakamokon zaben na ko wata Jiha, ba wai a bada sakamakon zaben a dunkule ba, a nasa bangare Faustin Boukoubi dake a matsayin mutum na biyu a Jam'iya mai mliki ya bukaci a watsa sakamakon zaben kamar yadda yake domin sabanin kuri'un da aka bayyana cikin Jahohi 9 na kasar ba kowa zai iya amincewa da shi ba.

Masu sharhi kan harakokin siyasa kasar na ganin cewa shakka babu madugun Jam'iyun adawar kasar Jean Pingzai bukaci a sake kilga kuri'un Jihar Haut –Ogooue dake a matsayin ma'aifa da kuma wurin da Shugaba mai ci Ali Bongo Dan Kabilar Teke yake da karfi, A yayin da aka bayyana cewa a sauren Jihohin kasar aka bayyana cewa kashi 60% na Al'ummar kasar ne suka fito zabe, amma hukumar zabe ta bayyana cewa a Jihar Haut –Ogooue kashi 93,99 suka gudanar da zabe kuma shugaba mai ci Ali Bongo ya samu kashi 95,5 na kuri'un da aka kada.

Wakilan kasashen Afirka da na kasashen Turai da suka je kasar domin sanya idanu kan yadda zaben ya gudana sun bayyana cewa a kwai matukar wuya, Al'ummar kasar su amince da wannan sakamakon zaben,to amma un ja hankalin jami'an tsaro da su tsaurara matakan tsaro na ganin an takaita tashin tashina don gudun sake jefa kasar cikin rikicin bayan zabe.jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben magoya bayan 'yan adawa sun bazu a kan tutunan birnin Libreville domin nuna rashin amincewar su da sakamakon zaben, a nasu bangare jami'an 'yan sanda suka yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa magoya bayan Jean Ping.amma duk da hakan saida suka kona majalisar dokokin kasar.Mazauna birnin Libreville sun ce, ta ko'ina ana iya hango hayaƙi ya tirniƙe yayin da dare ya soma shigowa.

Tun a shekara ta 2009 ne dai shugaba Ali Bongo Odinba ya dare shugabancin kasar ta Gabon bayan rasuwar mahaifinsa, a cikin shekaru bakwai din da ya yi yana gudanar da milki a kasar Shugaba Bongo ya yi kokarin karfafa kansa, amma duk da hakan Al'ummar kasar na adawa da milkinsa Iyalan gidan Bongo dai sun kwashe kusan rabin ƙarni suna mulkin kasar ta Gabon. ko mi take zama dai, abin da zai faru nan gaba shi fayyace makomar kasar domin dukkanin kungiyoyin kasa da kasa sun bayyana cewa shakka babu an tabka magudi a wannan zabe, hatta da kasar Faransa wacce ta yiwa kasar milkin mallaka kuma abokiya ta kut da kut ta Gwamnatin Bongo ta soki wannan sakamakon zaben.