Rashin Tsaro A Kasar Gabon Bayan Zaben Shugaban Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10459-rashin_tsaro_a_kasar_gabon_bayan_zaben_shugaban_kasa
An Kone Ginin Majalisar Dokokin Kasar Gabon
(last modified 2018-08-22T06:58:52+00:00 )
Sep 02, 2016 01:52 UTC
  • Rashin Tsaro A Kasar Gabon Bayan Zaben Shugaban Kasa

An Kone Ginin Majalisar Dokokin Kasar Gabon

"Yan hamayyar Siyasa A Kasar Gabon  Sun Kone ginin Majalisar dokokin kasar, a boren da su ke yi  na kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa.

Tashar telbijin din France 24 ta ce; tun daga lokacin da aka sanar da cewa shugaban kasa mai ci Ali Bango ne ya lashe zabe, 'yan hamayyar siyasa su ka ki amincewa tare kuma da yin tarzoma.

Babban birnin kasar ta Gabon, libreville ya fuskanci rikici da kone-kone a tsawon jiya alhamis, tare da jikkata mutane da dama.

Shugaban 'yan hamayya Jean Ping ya bayyana rashin amincewarsa da sakamakon zaben, wanda ya bayyana da cewa, yana cike da magudi.