An hana yin Zanga-zanga A Kasar Zimbabwe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10462-an_hana_yin_zanga_zanga_a_kasar_zimbabwe
"Yan sandan kasar Zimbabwe Sun hana yin zanga-zanga
(last modified 2018-08-22T06:58:52+00:00 )
Sep 02, 2016 01:54 UTC
  • An hana yin Zanga-zanga A Kasar Zimbabwe

"Yan sandan kasar Zimbabwe Sun hana yin zanga-zanga

Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya nakalto babban jami'in 'yan sandan birnin Harare na kasar Zimbabwe, Newbert Saunyama yana cewa; An hana yin Zanga-zanga daga nan har zuwa ranar 16 ga watan Satumba mai zuwa.

Jami'in 'yan sandan ya ci gaba da cewa an hana zanga-zangar ne domin basu da isassun jami'an tsaro da za su tabbatar da tsaro.

A ranar larabar da ta gabata 'yan hamayyar siyasa sun gudanar da zanga-zangar yin kira ga shugaban kasar Robert Mugabe da ya yi murabus. Masu zanga-zangar sun nuna rashin jin dadinsu akan tabarbarewar tatalin arziki da kin cika alkawalin gwamnati na magance shi.