Gwamnatin Somaliya Ta Dauki Aniyar Karfafa Sojojinta
Sep 02, 2016 06:26 UTC
Kudurin Somaliya Na Karfafa Randunar Sojanta.
Ma'aikatar tsaron kasar Somaliya ta bayyana aniyarta na karfafa sojojin kasar domin fada da ayyukan ta'addanci.
A wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar ta Somaliya ta fitar a jiya a alhamis, ta ce; Daga nan zuwa karshen shekarar nan da ake ciki, za a dauki karin sojoji 500. Sanarwar ta ci gaba da cewa da kasar tana da bukatuwa da karin sojoji domin bunkasa harkokin tsaro da kuma fada da ta'addanci.
Kungiyar al-shabab ta kai wani mummunan hari a ranar talatar da ta gabata a kusa da fadar shugaban kasa,wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 22 da kuma jikkata wasu 50.
Tags