Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar Rwanda Domin Fada Da Ta'addanci.
Matakan Tsaro A Kasar Rwanda Na Kokarin Tabbatar Da Tsaro
Cibiyar watsa labaru ta Africa Times ta ambata a jiya alhamis cewa; Kawo ya zuwa yanzu dai kasar ta Rwanda ba ta fuskanci harin ta'addanci ba, amma dai gwamnatin kasar ta bada umarni ga kananan hukumomi da su dauki tsauraran matakai a cikin cibiyoyin al'umma.
A watannin baya mai dai yan sandan kasar ta Rwanda sun gudanar da wani atasaye na fada da 'yan ta'adda da kuma hana kafuwar kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin kasar.
Wani jami'in gwamnatin kasar ta Rwanda, Francis Kaboneka, ya yi ishara da yadda ake da kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin kasashe daban-daban na Afirka da kuma na 'yan tawaye, ya yi gargadi akan wajabcin daukar matakai masu tsauri domin tabbatar da tsaro.
Kasashen Libya da Najeriya da Nijar, da Kamaru a Somalia suna daga cikin kasashen da su ke fama da matsalar 'yan ta'adda.