Najeriya : 'An Sace ma'aikatan Mai 15 A Fatakwal
'Yan Sanda A Najeriya sun ce an sace wasu ma'aikatan mai su guda 15 a yankin Fatakwal dake kudancin kasar.
Wasu mayaka ne da ba'a san ko suwa ne ba suka sace ma'aikatan su 14 tare da direbansu a jiya Juma'a suna akan hanyarsu ta zuwa Omoku/ Elele.
Mayakan dai sunyi harbi sama dan tsoratarda masu wucewa, kafin daga bisani suyi awan gaba da mutanen kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar Rivers Nnamdi Omoni ya tabbatarwa da kanfanin dilancin labaren AFP na Faransa.
Mr Omoni ya kara da cewa ana cikin farautar 'yan bindiga da kuma ma'aikatan su guda 15 da aka sace.
Wadanda lamarin ya shafa dai ma'aikatan kanfanin Nestoil ne dake kan hanyar zuwa offishinsu dake yankin Fatakwal.
Sace-sacen mutane don neman kudin fasan ba sabon abu ne ba a yankunan dake da arzikin man fatur a wannan kasa ta Najeriya mafi yawa attajirai ko ma'aikata 'yan kasahen waje don neman kudin fansa.