Zimbabwe : Mugabe Ya Jaddada Wajibcin Haramta Zanga-zanga
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya jaddada wajibcin haramta duk wata zanga-zangar 'yan adawa a Harare babban birnin kasar.
Mr. Mugabe wanda ke bayyana hakan a wani jawabi gaban matasa magoya bayan jam'iyyarsa ta Zanu PF ya ce '' Abun ya isa haka'' ba za'a ci gaba da sa iddo ana kallon masu son rushe tsarin demokuradiyya ba,
Dama kafin hakan 'yan sanda a kasar sun sanar da haramta duk wata zanga-zanga a birnin Harare har na tsawan makwanni biyu.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan adawa a wannan kasa suka zazafa zanga-zangar kyammar gwamnatin shugaba Robert Mugabe wace ko a makon daya gabata ta rikide zuwa rikici tsakanin jam'ian tsaro da masu zanga-zangar.
Shugaba Mugabe dai na zargin 'yan adawa kasar da neman wargaza mulkinsa bisa goyan bayan kasashen yamma.
'Yan adawa a kasar Zimbabuwe bna zargin Mugabe da jefa kasar cikin mawuyacin hali da tabarbarewar tattalin arzikin kasar.