Bukatar Shugaban kungiyar Alkalan kasar Gabon daga Magabatan Shara'ar kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10558-bukatar_shugaban_kungiyar_alkalan_kasar_gabon_daga_magabatan_shara'ar_kasar
Shugaban kungiyar Alkalan kasar Gabon ya bukaci magabatan mashara'antar kasar da su kare hakin Mutanan da aka kama sanadiyar tashe-tashen hankulan bayan zabe.
(last modified 2018-08-22T06:58:52+00:00 )
Sep 04, 2016 01:17 UTC
  • Bukatar Shugaban kungiyar Alkalan kasar Gabon daga Magabatan Shara'ar kasar

Shugaban kungiyar Alkalan kasar Gabon ya bukaci magabatan mashara'antar kasar da su kare hakin Mutanan da aka kama sanadiyar tashe-tashen hankulan bayan zabe.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Jean-Pierre Eva Luna Shugaban kungiyar Lauyoyin Kasar Gabon a jiya Assabar na cewa muna bukatar Jami'an tsaro gami da masu shara'a da su yi mu'amar mai kyau da wadanda aka kame sandiyar tashe-tashen hankulan bayan zabe.

Jean-Pierre  Eva Luna ya ce daga lokacin da aka bayyana sakamakon zaben shugabancin kasar a ranar Larabar da ta gabata  zuwa yanzu kimanin Mutane 800 aka kame a birnin Livraville , a sauren yankunan kuma sama da Mutane 300 aka kame kuma dukkanin su na cikin mawuyacin hali a gidajen yarin da ake tsare da su.

Shugaban Lauyoyin ya kara da cewa a halin da ake ciki Lauyoyin kalilan ne suka samu damar ganawa da wadanda ake tsare da su din, kuma ya zuwa yanzu, a birnin Livraville kawai Lauyoyi 120 suka suka rubuta sunan su domin kare wadanda aka kaman.