Bukatar Shugabannin Addinin Sudan ta kudu na kai Dakarun MDD birnin Juba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10561-bukatar_shugabannin_addinin_sudan_ta_kudu_na_kai_dakarun_mdd_birnin_juba
Shugabannin Addini na kasar Sudan ta kudu sun bukaci da a tura Dakarun wanzar da zaman Lafiya na MDD zuwa birnin Juba
(last modified 2018-08-22T06:58:52+00:00 )
Sep 04, 2016 01:18 UTC
  • Bukatar Shugabannin Addinin Sudan ta kudu na kai Dakarun MDD birnin Juba

Shugabannin Addini na kasar Sudan ta kudu sun bukaci da a tura Dakarun wanzar da zaman Lafiya na MDD zuwa birnin Juba

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a jiya Assabar Shugabanin Addini na kasar Sudan ta kudu sun tattauna da Jakadu 15 na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a birnin Juba, inda suka bukaci Kwamitin da ya tura Dakarun wanzar da zaman Lafiya  zuwa birnin Juba, domin goyon bayan fararen hula a yankunan da ake rikici.saidai Gwamnatin Sudan ta kudu ta bayyana adawar ta da tura Dakarun wanzar da zaman lafiyar zuwa cikin kasar.

A watan Yulin da ya gabata ne wani sabon rikici ya barke tsakanin Sojojin dake biyayya ga Shugaba Salva Keiir tare da na mataimakin sa na farko Riek Machar, lamari da ya yi sanadiyar mutuwar Sojoji da kuma fararen hula masu yawa tare kuma da gudun hijrar na duban fararen hula zuwa kasashen dake makobtaka da kasar.

Kimanin 'yan kasar Sudan ta Kudu dubu hudu da dubu 800  dake a matsayin rabin mutanan kasar  ne ke fuskantar karamcin abinci sanadiyar fari da kuma yakin basasar da kasar ke fuskanta.