Gwamnatin Kasar Italai Ta Kori Limamam Masallatai Guda Biyu Daga Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10582-gwamnatin_kasar_italai_ta_kori_limamam_masallatai_guda_biyu_daga_kasar
Gwamnatin kasar Italia ta bada sanarwan korar limamam masallatai guda biyu yan asalin kasashen Tunisia da Morroco daga kasar.
(last modified 2018-08-22T11:28:52+00:00 )
Sep 04, 2016 12:20 UTC
  • Gwamnatin Kasar Italai Ta Kori Limamam Masallatai Guda Biyu Daga Kasar

Gwamnatin kasar Italia ta bada sanarwan korar limamam masallatai guda biyu yan asalin kasashen Tunisia da Morroco daga kasar.

Shafin yanar gizo na al-alam ya nakalto ministan harkokin cikin gida na kasar Italia Anjulino Olfanu yana fadar haka a yau Lahadi, ya kuma kara da cewa limaman guda biyu suna yada tsatsauran ra'ayin addini a jawabnasu da kuma khudubobin da suke gabatarwa a garin Nuwaro na kasar.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar Italia ta kori limamim masallatai 11 daga kasar saboda yada tsatsauran ra'ayin addini tun shekara ta 2015.